A safiyar yau din nan ne a wata ganawa da daruruwan zakauعn wasanni daban-daban na wasannin Olympics da kuma wadanda suka cinye lambar yabo ta gasar wasannin Olympics ta duniya, Ayatullah Khamenei Jagoran juyin juya halin Musulunci ya kira wadannan Nambobin Yabo a matsayin wata alama ta ci gaba da bayyanar da karfin kasa tare da jaddada cewa: Kun tabbatar da cewa matasan Iran abin alfahari a matsayin "alamar koyi ta al'umma" wanda wannan ke nuna suna da karfin tabbatuwa kan tsororuwar manufa wanda ya janyo tunanin da idanunn duniya ga hasken Iran.
Haka nan kuma Jagoran juyin juya halin Musulunci ya yi ishara da cin zarafi da shirmen da shugaban kasar Amurka ya yi a baya-bayan nan yana mai cewa: Wannan mutumi ya yi kokarin farantawa sahyoniyawan rai da kuma bayyana kansa da irin halayensa ababen kyama da kuma karairayi masu yawa game da yankin da Iran da kuma al'ummar Iran, amma idan yana da iko to ya je ya kwantar da hankalin miliyoyin al'ummar kasar da suke ta rera taken kiyayya a kansa a dukkan jihohin Amurka.
Da yake bayyana jin dadinsa da kasancewa cikin matasa masu karfi wadanda bisa kokarinsu da jajircewarsu suka sanya al'umma farin ciki da kuma kishin matasa a fagen wasanni da kimiyya, ya ce: Lambobin yabon da kuka samu suna da daraja biyu akan lambobin yabo na wasu lokuta, domin kun ci nasara a cikin wani yanayi da makiya suke kokari cikin yakin ruwan sanyi su dankwafar tare da sanyawa al'umma damuwa ko ya zamo ya dankwafar da damaramkin da suke da ko suma watsar da yin yunkuri gwiwowyins su karye, amma kuma ku ka ba mai masa martani da karfin gwiwa ta hanyar nuna masa karfin al’umma a fagen aiki.
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya yi ishara da wasu daga cikin wasiwasin rashin samun fata da ake yadawa ga matasan kasar a matsayin kalaman da ba a akan sanayya ake yinsu ba’ tare da jaddada cewa: Iran madaukakiya da matasanta "Alama Ne Na Fata", kuma wajibi ne mu fahimci wannan muhimmin lamari cewa matasan Iran tare da iko da kwarewar kaiwa ga kololuwa; kamar yadda kuka kai ga kololuwa a duniya a fagen wasanni da kimiyya.
A yayin da yake ishara da ci gaban da aka samu a wasu bangarori bayan juyin juya halin Musulunci, Ayatullah Khamenei ya kara da cewa: Misali daya shi ne nasarorin da kuka samu a wannan shekara, wadanda watakila ba a taba samun irinsu ba a tarihin wasanni a kasar.
A yayin da yake murnar kaiwar matasa masu hazaka na kasar zuwa kololuwar kimiyya a duniya, ya ce: Wadannan ayyukan naku sun kara daukakar al'ummar Iran da kuma jawo hankali ga Iran.
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya kira "girmama tuta da yin sujada da addu'a ga 'yan wasan da suka samu nasara" da alamar shaida ce ta al'ummar Iran sannan ya kara da cewa: Masoyanmu matasa 'yan wasan Olympics a yanzu sun zamo tauraro mai haskakawa, kuma bayan shekaru goma idan suka ci gaba da kokarinsu to za su zama rana mai haskakawa, kuma aikin hukuma a wannan fanni yana da muhimmanci.
Ayatullah Khamenei ya dauki matsayin matasa a matsayin mai ci gaba da gudana bayan nasarar juyin juya halin Musulunci yana mai cewa: A cikin shekaru 8 da aka shafe ana yakin basasa, matasa ne suka aiwatar da irin wadannan ayyuka duk da karancin kayan ayyuka dayawa da rashin komai hannunsu amma sun samar da tsari da kayyakin tsaro, wanda hakan ya sa Iran ta samu nasara a kan makiya da ke da isasshen kayan aiki da aka tabbatar da su da kuma goyon bayan dukkan bangarori.
Ya dauki fagen daga na ilimi a matsayin wani fage na abin alfahari ga matasan kasar, yana mai ishara da kasancewar Iran a cikin manya-manyan bincike da darajojin kimiyya goma a duniya a fagage daban-daban da suka hada da "Nano", "Laser", "Nuclear", "Sana'o'in soji iri-iri" da "ci gaban likitanci", ya ce: Kwanaki kadan da suka gabata, na ji labari mai matukar muhimmanci cewa wata cibiyar bincike ta samu nasarar samun hanyar magance wata cutar da ke da wahalar magani a kasar.
Haka nan kuma yayin da yake tunawa da irin ayyukan da makiya suke yi na hana ci gaban ilimi daban-daban a Iran, Ayatullah Khamenei ya ce: Haka nan makiya al'ummar Iran suna kokarin sanya yanayin Iran cikin duhu da hargitsi ta hanyar "inkari ko yin watsi da wasu nasarori," "jirkitar da gaskiya da karya," "cika baki akan wasu batutuwa," da "farfaganda" da aka yi niyya, amma ku kuma ta hnayar tsayawa tsayin daka da kaiwa ga kololuwar wasanni da ilimi kun nuna duniya hasken da Iran ke da.
Ya kira rasa imani da ikon iyawa a matsayin daya daga cikin hanyoyin da makiya suke bi wajen bata al’umma da matasa masu tasowa sannan ya jaddada cewa: Sabanin wadannan ayyuka, matasa masu dogaro da karfin dakarun da ba su karewa, ya kamata su kara himma da kokarinsu na samun nasara, da samar da fata, da bayyanar da ikon al’umma.
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya yi ishara da kokarin da matasa suke yi na sadaukar da basirarsu ga al'ummar Iran da muhimmanci, ya kuma kara da cewa: Wasu na iya fatan rayuwa a wata kasa, to amma ya kamata wadannan mutane su gane cewa duk wani ci gaban da suka samu a wasu kasashen, to su baki ne; Yayin da Iran ta zama taku ce, da tsatsanku kuma ta zamo "ƙasa da gidanku".
Your Comment